IQNA

Azhar Ba Ta Amince Da Buga Wani Littafi Mai Bayani Kan Kur'ani Ba

15:50 - September 29, 2009
Lambar Labari: 1831603
Bangaren kasa da kasa; Kwamitin kula da harkokin bincike na jami'ar Azhar ya bayyana cewa jami'ar ba ta amince da buga wani littafi da ke bayani kan ayoyin kur'ani da harshen turanci ba.
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga jaridar kasar Saudiyya ta Madina a shafinta na internet cewa; Kwamitin kula da harkokin bincike na jami'ar Azhar ya bayyana cewa jami'ar ba ta amince da buga wani littafi da ke bayani kan ayoyin kur'ani da harshen turanci ba. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar kwamitin wajen daukarwannan mataki ita ce la'akari da aka yi kan rashin yin daidaito a cikin maganganun da bayanai da littafin ya kunsa, wanda hakan ya sabawa mahanga ta musulunci a fahimtar malaman jami'ar ta Azhar. 470716
captcha