IQNA

Jami'ar AlMustapha (SWA) Al'alami Za Ta Gudanar Da Gasar Kur'ani Da Hadisi

13:48 - November 01, 2009
Lambar Labari: 1843298
Bangaren kur'ani : jami'ar Almustapha (SWA) al'alami za ta gudanar da gasar kur'ani da hadisai a matakin share fage a gasar kasa da kasa ta Olumpik na Kur'ani da Hadisi.
Isma'il BirNiya babban mai kula da wannan gasar ta olumpik din kur'ani da hadisi da jami'ar Almustapha (SWA) al'alami take shiryawa a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna a birnin Qum ya bada labarin a wannan gasar mutane arba'in da biyar ne a lardunan jami'ar Almustapha (SAW) al'alami za su halarci wannan gasar. Daga cikin lardunar kuwa akwai kasashen Iraki,Afganistan,da Pakistan. Ya kara da cewa; a wannan gasa a matakin farko ta hanyar karatu ne kafin a kai ga jarrabawa ta hanyar rubutu da hardar kur'ani da bincike da addu'o'I da wakokin Musulunci da hadisai.

485620
captcha