Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Nasij ta watsa rahoton cewa; A birnin Makka ne komitin zartar na komitin hadin kan kungiyoyin duniya zai gudanar da taro kan mu'ujizar kur'ani da Sunna a ilmance. Kuma za a gudanar da wannan zama ne karkashin shugabancin Abdullah bin Abdulmuhsin Alturki babban sakataren hadin kungiyoyin Musulunci na duniya kuma mamba a komitin malumman Saudiya a Makkah. Abdallah bin Abdul Aziz Almusalih babban komitin ya bayyana cewa: a wannan zama za su tattauna da bincike kan abubuwa da suka shafiayyukan da suka gudanar da shirye-shiryen da za su aiwatar a nan gaba ta fuskar ilimin kur'ani.
540742