Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari day a nakalto daga kafofin yada labaran kasar Iraki an habarta cewa, jami'ar birnin Kufa ta nazarin fikihun Musulunci za ta gudanar da wata gasar bincike kan ilmomin kur'ani mai tsarki a matsayi na kasa da kasa. Wannan dai yana daya daga cikin irin namijin kokari da wannan jami'a take gudanarwa a lokaci zuwa lokaci. 545992