Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Saudiya SPA ta watsa rahoton cewa; a birnin Saopolo na kasar Brazil ne za a gudanar da taro kan kur'ani mai girma da kuma sunar ma'aikin (SWA). Kuma daga cikin mahalarta wannan taro akwai wakilan kasashen latin Amerika da na yankin Karabiya kuma sun jaddada wallafa littafai da harsunan Spaniyanci da Portigal da suka shafi kur'ani mai kirma da kuma sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka.
550490