IQNA

Wa'azin Kur'ani Da Farisanci A Indiya Na Nuni Da Karfin Al'adun Iraniyawa

13:06 - March 11, 2010
Lambar Labari: 1896830
Bangaren ilimi da nazari: wallafawa da yin wa'azi da harshen farisanci a kasar Indiya na nuni da yadda al'adun Iraniyanci ya yadu a wannan kasa.
A wata tattaunawa ce da Karim Najafi mai kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar Indiya ya yi da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a lokacin da yake halartar taron fahimtar juna da karawa juna sani na hukumar da ke kula da yada al'adun Iran a ketare ya bayyana cewa; wallafawa da yin wa'azi da harshen farisanci a kasar Indiya na nuni da yadda al'adun Iraniyanci ya yadu a wannan kasa. Ita dai kasar Indiya tana da kimanin mutane biliyan daya da miliyon dari biyu da kuma kimanin miliyon dari biyu musulmi ne . Da kuma ta kunshi al'adu iri daban-daban.

551096
captcha