IQNA

Ayatullahi Kablan Ya Bukaci Turkiya Da Ta Karfafa Danganta Da kasashen Musulmi

13:04 - March 11, 2010
Lambar Labari: 1896839
Bangaren siyasa da zamantakewa; Ayatullahi Kablan mukaddashin shugaban majalisar koli ta yan shia'a a kasar Labanon ya bukaci kasar Turkiya da ta karfafa dangantakarta da sauran kasashen musulmi da saura abubuwa da suka shafi amfanin muslmi.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga kasar Labanon bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Almanar ta watsa rahoton cewa; Ayatullahi Kablan mukaddashin shugaban majalisar koli ta yan shia'a a kasar Labanon ya bukaci kasar Turkiya da ta karfafa dangantakarta da sauran kasashen musulmi da saura abubuwa da suka shafi amfanin muslmi. Kuma ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da jakadan kasar Turkiya a kasar Labanon inda a wannan ganawar suka tattauna matsalolin da ke addabar kasashen musulmi da musulmi a fadin duniya da kuma hanyoyin magance irin matsalolin da suka tattauna a kai.

550766

captcha