IQNA

An Bada Shawarar Sanyawa Watan Ramadan Suna Watan Duniya na Kur'ani Mai Girma

14:34 - March 13, 2010
Lambar Labari: 1897478
Bangaren kasa da kasa; Muhammad Damyati masani kan harkokin kafafen watsa labarai a Saudiya a lokacin wani shiri na radiyo a Masar ya bada wannan shawara.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna bayan ta nakalto daga jaridar kasar Saudiya Ukaz ta watsa rahoton cewa; Muhammad Damyati masani kan harkokin kafafen watsa labarai a Saudiya a lokacin wani shiri na radiyo a Masar ya bada shawarar sanwa wata Ramadan sunan wata Kur'ani mai girma a fadin duniya da kuma yadda za mu rika yin koyi da kur'ani a rayuwarmu ta yau da kullum. A lokacin wannan tattaunawa dai ya bayyana irin mu'ijizojin da kur'ani ya kumsa ta fuskoki daban daban basu musaltuwa da lissafuwa.

551563

captcha