IQNA

Za A Gina Wata Madaba'antar Kur'ani A Kasar Kuwait

11:49 - March 16, 2010
Lambar Labari: 1898938
Bangaren kasa da kasa; za a gina wata babbar madaba'antar kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait domin gudanar da ayyuka na buga littafan kur'ani mai tsarki a kasar,
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, za a gina wata babbar madaba'antar kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait domin gudanar da ayyuka na buga littafan kur'ani mai tsarki a kasar, wanda babbar cibiyar kula da ayyukan kur'ani tare da yada ailiminsa a kasar, ita ce ta dauki nauiyin gudanar da ayyukan gina wannan babbar madaba'anta a kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa da zaran an kammala aikin ginin za a fara ayyukan buga kur'ani. 553077



captcha