Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Za a kara yawan kyautukan da ake bayarwa a gasarkaratu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasar Kuwait, Ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar wadda ita ce tare da hadin gwiwar hukumar kula da harkokin kur'ani ta kasar sukeshiriya irin wannan gasa, suka sanar da hakan a cikin wani bayani na hadin gwiwa da suka fitar a jiya. Bayanin ya ci gaba da cewa, yanzu haka dai an kammla dukkanin shirye-shirye da suka kamata na bayar da kyautukan wannan shekara. 553111