Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga APS ta watsa rahoton cewa; masu koyar da yara kanana karatun kur'ani a kasar Senegal sun bukaci da a tallafawa makaranta da binkasa wannan lamari tare da gwamnatin wannan kasa ta Senegal.Abdalla Gai shugaban daya daga cikin makarantun koyar da Kur'ani a kasar Senegal dangane da wannan labari ya bayyana cewa; a kokarinsu na ganin sun inganta koyar da karatun Kur'ani sun bullo da wani tsari na koyar da shi a cikin yaruka uku larabci ,faransanci da harshen gida.
556500