Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga kamfanin dillancin labaran rasid an bayyana cewa, Majalisar dokokin kasar Saudiyya ta gudanar da wani zama kofa rufe domin bahasi kan wata doka dake tabbatar da laifin duk wani malami da ya fitar da fatawar kafirta musulmi, kamar yadda malaman wahabiyawan kasar suke yi. Bayanin ya kara da cewa, da dama daga cikin malaman wahabiyan kasar Saudiyya suna kokarin suna bakin ganga dangane da abin da wasunsu ke yi, na kafirta sauran musulmi da ba wahabiyawa ba. 558907