IQNA

Taro Kan Sabbin Hanyoyin Habbaka Tattalin Arziki A Malazia

20:42 - April 11, 2010
Lambar Labari: 1905565
Bangaren kasa da kasa; Ana ci gaba da gudanar da wani zaman taro kan habbaka sabbin hanyoyi tattalin arziki na kasashen musulmi a birnin Kualalampour na kasar Malazia.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto day a nakalto daga kamfanin dillancin labaran 6thwief an bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da wani zaman taro kan habbaka sabbin hanyoyi tattalin arziki na kasashen musulmi a birnin Kualalampour na kasar Malazia. Bayanin ya ci gaba da cewa taron yana samun halartar masana kan harkokin tattalin na wasu daga cikin kasashen musulmi, da kuma malaman jami;a a birnin na Kualalampour. An kaddara mahalarta taron da cewa sun haura mutane dubu biyu. 560051
captcha