IQNA

An Gudanar Da Taron Kara Wa Juna Sani Kan Kur'ani

20:39 - April 20, 2010
Lambar Labari: 1910338
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani da aka yi wa taken birnin Kur'ani, wanda cibiyar kula da aharkokin ilmi da ala'adun kasashen musulmi ta shirya a Tehran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, An gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani da aka yi wa taken birnin Kur'ani, wanda cibiyar kula da aharkokin ilmi da ala'adun kasashen musulmi ta shirya a Tehran. Bayanin ya ci gaba da cewa wakilai daga sashe daban-daban na kasshen musulmi sun halarci zaman taron, inda aka tattauna muhimman lamurra day a kamata musulmi su mayar da hankali kansu da kuma yin riko da koyarwar kur'ani mai tsarkia cikin dukkanin bangarori na rayuwa ta zamantakewa da siyasa, da kuma harkoki na tattalin arziki. 565103


captcha