Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Za a gudanar da wani zaman taron hadin gwiwa tsakanin hukumar kare hakkokin mata da kanan yara ta duniya da kuma kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adun kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa, hukumar UNISCI da kuma kungiyar ISESCO dukkaninsu suna taka rawa wajen gudanar da ayyuka da suka yi kama da juna a wasu bangarori. Daga ciki kuwa hard a tsayawa kai da fata wajen kare hakkokin fararen hula da ake zalunta ko danne musu hakkoki, musamman ma kanan yara da mata daga cikinsu. 564934