Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran rasid na kasar Saudiyya cewa, ministan harkokin cikin kasar Saudiyya Naif dan Abdulaziz ya ki amincewa da duk wani batun bude masallatan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah, wanda a lokutan baya gwamnatin kasar tare da fatawr malaman wahabiyan kasar ta rufe a yankunan gabacin kasar. Baynain ya ci gaba da cewa ministan ya sanar da hakan ne sakamakon kiraye-kirayen da malaman addinin muslunci suke ci gaba da yi ne a sassa daban-daban na duniya tare da yin Allah wadai da wannan mummunan aiki da gwamnatin wahabiyan saudiyan take aikayawa kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah. 564883