IQNA

Ana Shirin Fara Gasar Hardar Kur'ani Ta Kasa A Malazia

20:37 - April 20, 2010
Lambar Labari: 1910344
Bangaren kasa da kasa; Ana shirin fara gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki ta kasa a kasar Malazia, inda daruruwan mahardata kur'ani na kasar za su kara da juna a jahar Malakai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalkto wani rahoto daga kamfanin dillancin labaran kasar Malazia Barnama cewa, Ana shirin fara gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki ta kasa a kasar Malazia, inda daruruwan mahardata kur'ani na kasar za su kara da juna a jahar Malakai. Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin wadanda za su shiga cikin gasar shekarunsu na tsakanin bakwai zuwa ashirin da biyar ne, kuma za a fitar da matsayi na daya da na biyu da na uku ne a dukkanin bangarorin da matakaida za a gudanar dagasar. 564937






captcha