Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran iba ya bada labarin cewa, bawahabiyan nan na kasar Saudiya Muhammad Uraifi da ya ci zarafin babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sistani ya dawo ya nemi uzuri.Muhammad Uraifi wanda daya ne daga cikin malaman wahabiya masu bayar da fatawa a kasar Saudiya, ya fitar da wani faifan kaset da aka saka sautinsa yana bayar da hakuri ga Sayyid Sistani, inda ya bayyana cewa bayan da aka nuna hotun gidan Sayyid Sistani da yadda ya ganshi, sai ya fahimci cewa lallai malami ne mai tsoron Allah da gudun duniya. Ya kirayi malaman sunna da su rika yin adalci dangane da malaman shi'a, maiamkon rufe ido akan kyawan dabi'u da halayensu. 564851