Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Za a fara gudanar da wani zaman taro da nufin kara bunkasa al'adun musulunci a kasashen musulimi, wanda za a gudanar a babban dakin taruka na cibiyar yada al'adun musulunci a birnin Ribat na kasar Morocco. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai mayar da hankali kan bahasi dangane da salon gini a tarihin musulunci da yadda aka kara fadada salonsa a lokutan baya, da yadda za a kiyaye shi a matsayin daya daga cikin ababen tarihin musulunci. 565731