Bangaren nazari:Bangaren rubuta makala a zamansa karo na ashirin da bakwai na gasar kasa da kasa ta Kur'ani mai girma ta ware bangarori uku na kur'ani ,da Ahlul Baiti (AS) na biyu Kur'ani da basira sai kuma na uku kur'ani da ilimomin dan adam.
Muhammad Muhrabi mai kula da lamuran da suka shafi makaloli a gasar kasa da kasa ta Kur'ani mai girma a wata tattaunawa day a yi da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta bayyana cewa; Bangaren rubuta makala a zamansa karo na ashirin da bakwai na gasar kasa da kasa ta Kur'ani mai girma ta ware bangarori uku na kur'ani ,da Ahlul Baiti (AS) na biyu Kur'ani da basira sai kuma na uku kur'ani da ilimomin dan adam. Bayan jin ra'ayin jama'a da shawartar malamai kwararru na Hauza da jami'a dam asana kan harkokin kur'ani da wadanda lamarin ya shafa sun e suka zabi wadannan bangarori guda uku.
561909