Bangaren siyasa da zamantakewa: a jiya ne talatin da daya ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara ne babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a wani zama da kungiyar ta gudanar a birnin Jidda na kasar saudiya ya fayyace ayyukan da kungiyar ta gudanar da yadda ta fuskanci haramtacciyar kasar Isra'ila kan zaluncin da take nunawa al'ummar Palsdinu da mamaye su.
Daga Reshenta na kasar Turkiya ne bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Ma'a cibiyar da ke kula da harkokin addini a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton : a jiya ne talatin da daya ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara ne babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a wani zama da kungiyar ta gudanar a birnin Jidda na kasar saudiya ya fayyace ayyukan da kungiyar ta gudanar da yadda ta fuskanci haramtacciyar kasar Isra'ila kan zaluncin da take nunawa al'ummar Palsdinu da mamaye su. Wannan zama yanada matukar muhimmanci musamman idan aka yi la'akari da yadda zalumtar al'ummar Palsdinu ya yi tsanani a yan shekarun nan da kuma yadda ake kara samun rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi da kasashensu alhali daya daga cikin dalilan kafa wannan kungiya ta kasashen musulmi shi ne kare masallacin Kudus da al'ummar Palsdinu.
566107