Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar Isesko ta watsa rahoton cewa; a kasar Beljuim ne za a ilmantar da malaman addini musamman malaman juma'a na masallatai a kasar kuma hukumar bada ilimi da horo ta Asesko da ke kula ta al'adun Musulunci za ta shirya daga ranar bakwai ga watan Ordebeshe zuwa goma da watan a Burukesel. Wannan shiri wata babbar dam ace da za ta taimaka wa malamai na addini kara sanin makamar aiki a fuskar yada addinin Musulunci a tsakanin al'umma musamman a nahiyar Turai.
567002