IQNA

A Turkiya An Kafa Cibiyar Bincike Ta Kur'ani

16:18 - April 26, 2010
Lambar Labari: 1913184
Bangaren kasa da kasa: ma;aikatar ilimi mai zurfi da harkokin addini a kasar Turkiya a daidai wannan lokaci na bayyana wannan shekara ta 2010 a matsayin shekarar Kur'ani mai girmata kuduri aniyar kafa wata cibiyar binciken ta kur'ani a birnin Istambul.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani anan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne bayan ta nakalto daga risalehaber ta watsa rahoton cewa; ma;aikatar ilimi mai zurfi da harkokin addini a kasar Turkiya a daidai wannan lokaci na bayyana wannan shekara ta 2010 a matsayin shekarar Kur'ani mai girmata kuduri aniyar kafa wata cibiyar binciken ta kur'ani a birnin Istambul. Muhammad Amin Ozafsar mai bawa ministan harkokin addini na kasar Turkiya a wata tattaunawa da manema labarai na wannan kasa ya bada wannan labari a wani mataki na kara karfafawa masu bincike kan ayoyin kur'ania jami'ai karfin guiwa.

568412

captcha