Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga turkiyegazetesi ta watsa rahoton cewa; mu'assisar bincike ta Gallup ta bayyana cewa: addinin Musulunci ya fi sauran addinai a duniya ci gaba da yaduwa.Karkashin binciken da aka gudanar da jin ra'ayin jama'a da wannan mu'assisar ta gudanar daga cikin biliyan bakwai na al'ummar duniya kimanin biliyan daya da rabi musulmi ne da ke rayuwa a sama da kasahen hamsin da bakwai na duniya yayinda wasu ke rayuwa a kasashe dab a nasu na asali ba dari dad a ashirin.
571351