IQNA

Shirin HKI Na Ruguza Kudus Ta Yin Ginin Karkashin Kasa

16:31 - June 14, 2010
Lambar Labari: 1939687
Bangaren manema labarai;Sheikh Teisiri Altamimi babban alkali a Palasdinu a wata tattaunawa kan wasu shirye-shiryen gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na makircin ruguza masallatin Aksa yana daga cikin shirinsu na mamaye birnin Kudus.


Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga cibiyar labarai ta Hauza ta watsa rahoton cewa; Sheikh Teisiri Altamimi babban alkali a Palasdinu a wata tattaunawa kan wasu shirye-shiryen gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na makircin ruguza masallatin Aksa yana daga cikin shirinsu na mamaye birnin Kudus.Sheikh teisir Altamimi ya kara da cewa; yahudawan sahyoniya sun kulla makirce makirce na maida masallacin kudus da kudus mai tsarki karkashin mamayensu. Kuma yana kiran kasashen musulmi da musulmi da su tashi tsaye domin magance wannan makirci da zagon kasan haramtacciyar kasar Isra'ila.


596373

captcha