Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan daga reshenta na kasar Labanon ta watsa rahoton cewa; mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmaya a kasar Labanon a ranar ashirin da biyu ga watan Khurdad a cikin wani jawabi da ya gabatar ya yi nuni da kokarin imam Khomeini ® na tabbatar da hadin kai a tsakanin al'umma kuma imam ne tutar hadin a wannan karni. Sheikh Na'im Kasim ya kara da cewa dan Palsdini da tsayin Dakar day a yi kan gwamgwarmya da yakar zalunci ya isa misali kan rawar da wannan bawon Allah ya taka.
596388