Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na uskudar cewa, an gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka yi wa lakabi da mafi kyawun kira'a akasar Turkiya, wadda aka gudanar a garin Uskudar na kasar. Bayanin ya kara da cewa babban kwamitin mahardata kur'ani na kasar Turkiya ne ya shirya gudanar da wannan gasa, inda daga karshe a ka zabi wasu makarnta biyu aka ba su kyautar lashe gasar. 597118