Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na iec.houstn an habarta cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Ali Naqi Hadi (AS) a jahar Texas ta kasar Amurka da ke samun halartar musulmi. Bayanin ya kara da cewa cibiyar da ke kula da harkokin musulmi a jahar musamman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) ita ce ta dauki nauyin shirya taron. 597874