Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar kula da rubuce-rubucen Musulunci cewa, daya daga cikin malaman jami'a a Iran kuma fitaccen marubuci Muhamamd Habibi ya bayyana cewa Israila ba za ta iya kawar da hankulan al'ummar duniya kan killace Gaza da take yi ba. Ya ci gaba da cewa Isra'ila tana zaton cewa ta hanyar sace jirgin ruwa da kashe wadanda ke cikinsa masu kai taimako a gaza za ta iya yaudarar duniya, wanda a cewarsa hakan babban kuskure ne take yi. 598124