Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da wani zaman taro da aka yi walakabi liyafar kur'ani mai tsarki a garin Mardin da ke kasar Turkiya wanda kunyar matasan yankin ta shirya gudanarwa. Bayanin ya kara da cewa a wajen taron an gudanar da karatun kur'ani wanda daruruwan mutane suka halarta, kamar yadda aka gabatar da bayanai kan alkur'ani mai tsarki. 598623