Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga jaridar kasar Katar Alshark ta watsa rahoton cewa; ana bada horo ga mata ma'aikata a muassisoshi da cibiyoyin hardar kur'ani mai girma a birnin Doha fadar mulkin kasar Katar kuma an fara ne a ranar ashirin da bakwai ga watan Khurdad na shekarar hijira shamsiya.Amina Abdullah Alibrahim babbar darektar darul Kur'ani mia girma a kasar Katar kan wannan llabari ta kara da cewa; Wannan wani mataki ne na farko na bada horo na musamman ga mata masu aiki a mu'assisoshi da cibiyoyi na kur'ani a fadin kasar ta Katar kuma haka zai zama tamkar kara masu karfin guiwa a aiki da suke gudanarwa a irin wadannnan cibiyoyi na kur'ani mai girma.
599541