IQNA

A Yau Ne Za A Bude Baje Kolin Rubuce-Rubucen Musulunci

16:54 - June 19, 2010
Lambar Labari: 1942495
Bangaren kasa da kasa; A yau ne aka bude babban baje koli na kasa da kasa kan rubuce-rubucen musulunci a birnin kazan na kasar Tataristan tare da halartar jami'an diplomasiyya gami da na gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na info-islam an bayyana cewa, a yau ne aka bude babban baje koli na kasa da kasa kan rubuce-rubucen musulunci a birnin kazan na kasar Tataristan tare da halartar jami'an diplomasiyya gami da na gwamnati. Bayanin ya ci gaba da cewa daga wadanda suka halarci bude wannan baje akwai mataimakin ministan ma'aikatar kula da harkokin musulunci na kasar Kuwait, gami da masana da jami'ai daga kasashen musulmi da na larabawa. 599611



captcha