Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani taro da aka gudanar kan yanayin gyara da kare mahalli, mataimakin shugaban kasa Muhammad Javad Muhammadizadeh tare da shugaban hukumar kula da mahalli na kasa sun jadda cewa, kur'ani mai tsarki shi ne babban abin da za a koma zuwa gare shi domin samun mafita dangane da yadda za a kiyaye mahalli tare da hakkokin zamantakewar jama'a. Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin bangarorin biyu sun jadda wajabcin yin aiki da koyarwar kur'ani mai tsarki a cikin dukkanin bangarori na rayuwa. 599441