Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wanda ya jagoranci sallar Juma a birnin Tehran ya bayyana cewa hijabi umurnin Allah da manzonsa ne, saboda haka dole ne a ganshi a cikin harkokin rayuwar zamantakewa. Bayanin ya ci gaba da cewa malamin ya jadda wajabcin yin riko da dukkanin koyarwar addinin muslunci a cikin rayuwar musulmi,ba yin riko da wani bangare da kuma yin watsi da wani bangaren wannan koyarwa ba. Ya tabbatar da maganarsa ta hanyar ambatar hadisai daga manzo da a'imma tsirar Allah ta tabbata ga manzon Allah daiyalan gidansa tsarkaka. 599664