Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yeni safak an bayyana cewa, mahardata kur'ani mai tsarki na birnin Istanbul na kasar Turkiya za su gudanar da wani zama inda za su tattauna muhimman batutuwa da suka danganci hardar kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar, da ma wadanda suke koyon karatu a makaratun Musulunci . 599796