Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na kasar an habarta cewa, babban malami mai bayar da fatawa a kasar Syria Shekh Badruddin Ahmad Hasun ya bayyana cewa Isra'ila ba ta girmama duk wasu ababe masu tsaki a cikin kowane addini ballantana mutuncin dan adam. Ya ci gaba da cewa abin da Isra'ila ta yin a kai hari a kan fararen hula masu hankoron kai agaji ga al'ummar Gaza ya isa ya zama babban misali kan hakan.600333