IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Sarki Kabus A Oman

19:54 - June 20, 2010
Lambar Labari: 1943333
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da gasar share fage ta babbar gasar karatun kur'ani mai tsarki da harda ta sarki Kabus na kasar Oman.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Omanobserver cewa, an fara gudanar da gasar share fage ta babbar gasar karatun kur'ani mai tsarki da harda ta sarki Kabus na kasar Oman, da za a gudanar a birnin Maskat fadar mulkin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar kula da al'adu ta kasar da ake yi wa lakabi da Sultan Kabus ita ce za ta dauki nauyin gudanar da wannan gasa. 600194




captcha