IQNA

Za A Gudanar Da Maulidin Imam Muhammad Taqi (AS) A Kutaif

13:34 - June 22, 2010
Lambar Labari: 1944550
Bangaren kasa da kasa; A yau ne za a gudanar da tarukan maulidin Imam Muhammad Taqi (AS) a masallacin Imam Hussein (AS) da ke garin wamiyya da ke lardin Kutaif a Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran rasid an habarta cewa, a yau ne za a gudanar da tarukan maulidin Imam Muhammad Taqi (AS) a masallacin Imam Hussein (AS) da ke garin wamiyya da ke lardin Kutaif a Saudiyya. Bayanin ya ci da cewa za a gudanar da taron ne yau tare da halartar manyan malaman addini na yankin da kuma daruruwan mutane da suke da bukatar halartar taron. 601476




captcha