Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga banagaren yada labaransa a kasar Jordan an habarta cewa, Babban jami'i mai kula da harkoki bunkasa ilmomin addini a lardin arbad na kasar Jordan ya bayyana cewa a cikin wannan bazarar an bude cibiyoyin harder kur'ani 126 a kasar. Ya ci gaba da cewa wadannan cibiyoyin sun fara yin rijistar sunayen dalibai, yayin wasu daga cikinsu ma tuni suka fara karatu tare da hardar kur'ani mai tsarki. Ya ce za a ci gaba da aiwatar da shirin, sakamakon karbuwar da yake samu a wajen al'ummar kasar. 601181