IQNA

An Bude Bangaren Horar Da Yara Karatun Kur'ani A Karbala

15:48 - June 23, 2010
Lambar Labari: 1945462
Bangaren kasa da kasa; An bude wata cibiya ta koyar da yara 'yan makaranta karatun kur'ani mai tsarki da ilmomin fikihu da akida a birnin Karbala mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kur'ani na muzn ya habarta cewa, an bude wata cibiya ta koyar da yara 'yan makaranta karatun kur'ani mai tsarki da ilmomin fikihu da akidar musulunci a birnin Karbala mai alfarma na kasar Iraki. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri bayar da horo zai kebanci kanan yara ne, zai kasance a matakan firamare da sakandare. An bude wannan bangare ne a cikin hubbaren Imam Hussain (AS) da ke cikin birnin mai alfarma.602439
captcha