Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar kasar Alwatan ta kasar Saudiyya an habarta cewa, za a bude wata bababr cibiyar kur'ani mai tsarki a garin Khamis Mushait na kasar Saudiyya da kimar kudi riyal miliyan goma, domin gudanar da ayyukan da suka danganci kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa bababn daraktan hukumar kula da harkoki da ayyuka da suka danganci kur'ani na kasar Saudiyya shi ne ya sanar da hakan, inda ya ce yanzu haka aikin gina cibiyar ya yi nisa. 603304