Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muhit cewa, babban daraktan cibiyar mabir kur'aniya ta kasar Kuwait ya bayyana cewa, za a fara gudanar da wani shiri na khatmar kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar za ta dauki nauyin shiryawa. Bayanin ya ci gaba da cewa bababr manufar gudanar da wannan shiri ita ce bayar da dama ga yara da kuma matasa da suke hutun bazara su yi amfani da lokacinsu wajen karatun kur'ani mai tsarki. 603269