IQNA

Matakin Karshe Na Gasar Kur'ani A Fadin Bangaldesh

15:47 - June 24, 2010
Lambar Labari: 1945790
Bangaren harkokin kur'ani: an kawo matakin karshe na gasar karatun kur'ani mai girma a fadin kasar Bangladesh da ofishin kula da yada al'adun Iran a wannan kasa ya shirya kuma a jiya ne aka kawo karshen wannan gasa ta karatun kur'ani.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshen cibiyar da hukumar kula da yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran da kara kusanci a tsakanin kasashen musulmi da musulmi a fadin duniya ta watsa rahoton cewa; an kawo matakin karshe na gasar karatun kur'ani mai girma a fadin kasar Bangladesh da ofishin kula da yada al'adun Iran a wannan kasa ya shirya kuma a jiya ne aka kawo karshen wannan gasa ta karatun kur'ani.Daga karshe dai mutane biyu ne suka yi sa'ar isa ga zagayen karshe na wannan gasar wadanda suka yi fafatawa mai karfi da hakan zai bas u damar samun daya daga cikinsu da zai yi sa'ar samun cancantar gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa karo na ashirin da bakwai a nan Tehran.


603290
captcha