IQNA

Kungiyar OIC Ta Gudanar Da Taron Matasa A Yankin Balkan

18:45 - June 24, 2010
Lambar Labari: 1945820
Bangaren kasa da kasa; Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta shirya gudanar da wani zaman taron matasa na yankin Balkan a birnin Istanbul na kasar Turkiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da banagaren yada labaransa na kasashen gabacin turai ya bayar an bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta shirya gudanar da wani zaman taron matasa na yankin Balkan a birnin Istanbul na kasar Turkiya. Bayanin ay ci gaba da cewa taron wanda ya samu halartar shugabannin kungiyoyin matasa na kasashen yankin Balkan, ya mayar da hankali ne kan irin rawar da matasa za su takawa a cikin rayuwar zamantakewar jama'a, tare da bayar da gudunmawa ga sauran matasa 'yan uwansu a dukkanin bangarori. 603493


captcha