Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da bangaren yada labaransa na lardin Isfahan ya bayar an habarta cewa, shugaban bangaren isar da sakon addinin Musulunci ya bayyana cewa tabligi da sadarwa ta harkokin addini tamkar cika aikin annabawa ne. Malamin ya ci gaba da cewa masu isar da sakon addini suna yin wa'azi tare da fadar da al'umma gami da ilmantar da ita hakikanin koyarwar addini, yayin da masu harkar sadarwa kian adini suke bayyana gaskiyar abin da ke faruwa da kuma shiryar da mutane. 603494