Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Fira ministan kasar Malzia ya kira ga dukkanin kasashen musulmi da su samar da wasu wurare na yin kayayyakin halal da za a iya yin amfani da su a ko'ina a duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa fira ministan kasar ta Malazia ya yi wannan kira a lokain da yake jawabi kan kayan da kasar ta ke samarwa, wanda ya jadda cewa ya rataya kan kasashen musulmi su kara bunkasa harkokin samar da kayan halal a Musulunci a kasashensu, ta yadda sauran musulmi da suke wasu wurare ma za su iya amfana da su. 604009