Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar zaman ta kasar Turkiya ta habarta cewa, bayan da kasashen Rasha da Amurka suka tura wakilansu a kungiyar kasashen musulmi ta OIC gwamnatin Birtaniya ma ta tura nata wakilin da zai wakilce ta a cikin kungiyar. Bayanin ya ci gaba da cewa musulma ta farko a cikin majalisar ministocin fira ministan kasar Birtaniya Kate Rodd, ita ce wakiliyar kasar a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, inda za ta ci gaba da wakiltar kasar a dukkanin tarukan da kungiyar take gudanarwa. 604088