IQNA

An Hana Gudanar Da Tarukan Maulidin Imam Ali (AS) A Masar

19:31 - June 27, 2010
Lambar Labari: 1946903
Bangaren kasa da kasa; Gwamnatin kasar Masar ta hana gudanar da tarukan maulidin Imam Ali (AS) a kasar Masar, a ciga da takura ma mabiya mazhabar shi'a na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar yaum sabi ta kasar Masar ta rubuta a shafin na yanar gizo cewa, gwamnatin kasar Masar ta hana gudanar da tarukan maulidin Imam Ali (AS) a kasar Masar, bayan da aka dauki matakan takura ma mabiya mazhabar shi'a na kasar. Jaridar ta ci gaba da cewa gwamnatin kasar ta tsananta irin matakan da take dauka na takura wa mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) musamman ma a cikin 'yan lokutan nan, inda ta kan tura jami'an tsaro a cikin fararen kaya domin kawo labarai kan ayyukan da suke gudanarwa da tarukan addini na raya tafarkin iyalan gidan manzo(SAW) tare da daukar matakan hana su. 604150




captcha