Ali Rida Kur'bani mai kula da shirye-shiryen wannan gasar ta kasa da kasa karo na sha shidda ta karatun kur'ani da Hadisin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarka da jami'ar Almustapha (SWA) al'alami a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ya bayyana cewa; an kara lokacin rubuta sunaye a gasar karatun Kur'ani da Hadisi da jami'ar Almustapha (SWA) al'alami ke shirya mai sunan olympik din gasar Kur'ani da hadisin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayansa tsarkaka.Wannan karin lokaci wata dam ace ga duk wanda yak e son shiga wannan gasar da kuma lokaci ne da hakan zai kara yawan wadanda za su rubuta sunansu a wannan gasar.
604797