IQNA

Kimanin Sansani 140 Na Kur'ani Aka Bude A Lardin Ukba Na Jodan

10:25 - June 28, 2010
Lambar Labari: 1947130
Bangaren harkokin kur'ani: shugaban da ke kula da harkokin addini a lardin Ukba na Jodan ya bada labarin bude tsangayar hardar kur'ani a Masallatai guda dari da arba'in da hudu.

Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta a kasar Jodan ta watsa rahoton cewa; shugaban da ke kula da harkokin addini a lardin Ukba na Jodan ya bada labarin bude tsangayar hardar kur'ani a Masallatai guda dari da arba'in da hudu. Sheikh Suleiman Balil ya kara da cewa; burin wannan tsangayar karatun Kur'ani da bude wadannan cibiyoyi shi ne karfafawa matasa karfin guiwar rungumar karatun kur'ani da bawa wannnan bangare mai muhimmanci matsayinsa na hakika a rayuwa da addini.


604564

captcha